Damuwa kan lafiyar shugaban Najeriya | Labarai | DW | 03.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Damuwa kan lafiyar shugaban Najeriya

Karo na uku a jere Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya gaza fitowa taron majalisar zartaswa ta kasa da ke gudana mako-mako.

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya sake tsallake taron majalisar zartaswa karo na uku a jere, abin da ke kara jita-jita game da rashin lafiyar shugaban. Ministan yada labarai Lai Mohammed ya kare matakin shugaban inda ya kaurace taro sakamakon shawara daga likitoci. Akwai damuwa game da yanayin lafiyar Shugaba Buhari dan shekaru 74 da haihuwa tun lokacin da ya koma gida a watan Maris bayan jinya a kasar Birtaniya.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranci taron. Gwamnatin Najeriya ta kawar da tsoro da ake nunawa bisa rashin lafiyar shugaban.