1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dambarwar siyasar Nijar na ƙara yin muni

October 8, 2013

'Yan majalisun dokoki na jam'iyyar Lumana Modem Afrika ta Hama Amadou Kakakin majalisar dokokin Nijar sun bi sahun jam'iyyun siyasa na adawa a zauren majalisar.

https://p.dw.com/p/19wFV
Wahlen im Niger. Kandidat Hama Amadou. Personen; Politik; Bundestagswahl; Wahlen; Niger; Präsidentschaftswahlen; Wahllokal; Afrika; Politiker; Präsidentschaftskandidat; Wahl; persons; politics; election; politicians; political; vote; B950_168021; B950; elections; contest; general; politician; poll;
Hoto: picture-alliance/Photoshot

Kimanin yan majalisun 25 na jam'iyyar suka bayyana wata sanarwa ta bin bayan sahun 'yan adawar.Hakan kuwa ya biyo bayan matakin da jam'iyyar ta ɗauka ranar 22 ga watan Agustan da ya gabata na ba da sanarwa ficewa daga ƙawance jam'iyyun siyasar masu goyon bayan gwamnati wato MRN.

Duk da ma Lumana ta fice daga ƙawance MRN na da 'yan majalisu 58

Ba shakka da sauran kallo a siyasar ta Nijar wacce aka daɗe ana yi wa kallon tana cike da rikici wanda sotari ya kan kan kai ga haddasa yamutsin da kan janyo kiferwa gwamnati.Dan majalisa Saidou Bakary,shi ne shugaban gungun 'yan majalisun Lumana.Ya ce: '' Demokraɗiyya dai ta tanadi adawa,saboda haka duk wani abin da ƙasa za ta ƙaru da shi to a shirye muke mu ba da haɗin kai,amma ba za mu yarda ba da abin da zai ƙwari ƙasa.''Suma ɓangaren masu rinjaye,Dan majalisa Asumana Malam Issa,na jamiyar PNDS Tarayya.Ya ce: ''lalle ficewar abokan su ba su ji daɗi ba,To amma suna da rinjaye kuma yanzu za su yi aiki kamar yadda yanayi ya ba da su 58,don akwai wasu 'yan majalisar da zasu kawo musu goyon baya.''

Gebäude des Parlaments der Republik Niger, Niamey. Foto: Mahaman Kanta/DW, 19.5.2011, Niamey / Niger, Zulieferer: Thomas Mösch
Majalisar dokokin NijarHoto: DW

Shin ko yaya za ta kaya a Majalisar dokokin ta Nijar

Shi dai shugaban majalisar dokokin 'yan majalisar ne ke zaɓensa a kan wa'adin shekaru biyar. A yanzu da yake ta fito fili shi shugaban majalisar yana ɓangaren adawa,ana kallon yadda zai tafiyar da aikin gwamnati.To ko wane tasiri wannan sabon kawancen zai kawo? Boukar Maina Karté,masani ne a fannin dokar tsarin mulki,kuma mai koyar wa ne a jami'ar Yamai. Ya ce:'' Akwai tasiri don dokoki wajen 40 gwamnati ta kawo majalisa za'a yi mahawara a kansu fiye da yadda ake maharawa a can da, Amma ya kamata su kauda siyasa waje ɗaya su yi wa ƙasa aiki.''A cikin tsarin kundin mulki ƙasar Nijar wanda ake aiki da shi shugaban majalisar dokoki shi ne mutun na biyu mafi girma muƙami wanda idan shugaban ya kau saboda wasu dalilai na rashin lafiya ko mutuwa to kam shi ne zai iya riƙe mulki kana ya shirya wani sabon zaɓe a cikin kwanaki 90.

epa02847783 President Mahamadou Issoufou of Niger during a meeting with US President Barack Obama and fellow African leaders from Niger, Benin, and Guinea, in the Cabinet Room of the White House, in Washington DC, USA, 29 July 2011. EPA/MARTIN H. SIMON / POOL +++(c) dpa - Bildfunk+++
Mahamadou Issoufou shugaban ƙasar NijarHoto: picture alliance / dpa

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto haɗe da hira da Garzali Yakubu ya yi da Dr Yahaya Janjuna wani mai yin sharhi a kan al'amura a Nijar dangane da rikicin siyasar ƙasar

Mawallafi : Mahaman Kanta
Edita : Abdourahamane Hassane


Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani