Dambarwar siyasa a jamiyyar NDC mai mulki a Ghana | Siyasa | DW | 07.07.2011
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Dambarwar siyasa a jamiyyar NDC mai mulki a Ghana

Bayyana anniyar tsayawa takarar shugaban kasa da uwargidan tsohon shugaban Ghana Jerry Rawlings ta yi na cigaba da janyo Takaddama a jamiyyar NDC mai mulki

Shugaba John Atta Mills na Ghana

Shugaba John Atta Mills na Ghana

Daga ranar takwas zuwa goma ga wannan wata jam'iyyar NDC dake mulki a ƙasar Ghana zata gudanar da babban taronta na fid da gwanin da zai jagoranci jam'iyyar a zaɓen ƙasar da za a gudanar a shekara ta 2012. Ana fata taron zai taimaka a raba gardama a tsakanin masu fafutukar jagorantar jam'iyyar su biyu Nana Konedu Agyman Rawlings da shugaba mai ci farfesa Atta Mills.

Mawallafiya: Ramatu Abubakar Mahmud/Pinado Abdu

Edita: Ahmad Tijani Lawal

Sauti da bidiyo akan labarin