Dambarwar siyasa a Iraki na ci gaba da janyo rashin tabbas | Siyasa | DW | 13.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Dambarwar siyasa a Iraki na ci gaba da janyo rashin tabbas

Yayin da ake ci gaba da fafatawa da mayakan Islama a wasu yankuna na Iraki, ana kara samun rashin jituwa tsakanin shugabannin siyasar kasar a birnin Bagadaza.

Firamnistan kasar Iraki Nuri al-Maliki na ci gaba da nuna turjiya bayan Shugaba Fuad Masum ya zabi wanda zai maye gurbinsa abin da ke kara jefa kasar cikin rashin tabbas, yayin da ake ci gaba da fafatawa da tsageru masu dauke da makamai.

Kasar ta Iraki ta shiga rikici mafi muni tun bayan janye dakarun Amirka a karshen shekara ta 2011. Rikicin siyasar kasar ya kara dagulewa saboda yadda Firamnistan mai barin gado Nuri al-Maliki ya ki amincewa da rungumar kaddara, bayan Shugaba Fuad Masum ya nemi Heidar al-Abadi ya kafa sabuwar gwamnati, wajen karbar mukamin na firaminista.

Rashin samun goyon bayan siyasa

Iran Rohani Irak al Maliki

Maliki da Rohani na Iran

Makili wanda ya gamu da cikas a neman wa'adi na uku na mulki, ya bayyana dalilan da ya sa aka zuba jami'an tsaro ko'ina a Bagadaza babban birnin kasar.

"Abin da nake jin tsoro shi ne yadda ake samun gungun 'yan al-Qaeda, da tsageru masu da'awar kafa daular Islama, da sauran tsageru ke daukan makamai da sunan kare Maliki ko wani abu. Wannan haramtaccen abu ne, saboda ana iya amfani da wannan dama wajen tayar da zaune tsaye, ta hanyar zuwa da motoci irin na jami'an tsaro, domin haka ya dace a tsaurara matakan tsaro musamman kan tawagar motoci."

Maliki ya ci gaba da rasa goyon baya daga jiga-jigan da ke mara wa jam'iyya mai mulki baya a ciki da wajen kasar. Kasashen duniya na fataa Heidar al-Abadi da aka zaba a matsayin sabon firamnista zai kafa gwamnati wadda za ta samu amincewar 'yan kasa, saboda tunkarar 'yan kungiyar tsagerun masu neman kafa daular Islama.

Takatsantsan waje daukar matakan soji

Gabriel empfängt Irfan Ortac 12.08.2014 Berlin

Sigmar Gabriel da Irfan Ortac a Berlin

Yayin da Amirka ta fara amfani da jiragen saman yaki a kan mayakan, abin da ya taimaka gaya wajen dakile musu hanzari musamman ta yankin Kurdawa, inda jami'an tsaron suka samu kwarin gwiwa na ci gaba da yakan tsagerun. A daya hannu Shugaban Faransa Francois Hollande ya amince da shirin ba da makamai ga Kurdawan, amma Sigmar Gabriel mataimakin shugabar gwamnatin Jamus ya nemi a yi takatsantsan, inda ya ce:

"Ina gani ya dace a yi takatsantsan kan wannan mahawara, saboda yawancin wadannan makamai kan ci gaba da kasancewa a wuraren da rikicin ya faru. Abin da ya faru a baya ya koya mana darasi a yankunan da aka samu rikice-rikice."

Sai dai Ursula von der Leyen da ke zama ministar tsaron Jamus, ta nunar da cewa akwai yiwuwar tura makamai, saboda yadda lamura ke kara sukurkucewa a kasar ta Iraki, tana mai cewa:

"A wannan lokaci muna aiki tsakanin ma'aikatar tsaro da ta harkokin waje, ba wai bayar da agajin jinkai ba kawai, har da kananan makamai."

Majiyoyin jami'an tsaro da na asibiti sun tabbatar da cewa wasu hare-hare da aka kai a wannan Laraba a birnin Bagadaza sun hallaka kimanin mutane 10, yayin da wasu fiye da 20 suka samu raunika.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Sauti da bidiyo akan labarin