1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bai wa el-Zakzaky izinin fita neman magani

Ramatu Garba Baba
August 8, 2019

Gwamnatin Najeriya ta bai wa Sheikh Ibrahim El-Zakzaky izinin zuwa kasar Indiya don neman lafiya bayan da jagoran ya kwashi sama da shekaru 3 a tsare.

https://p.dw.com/p/3NaDh
Nigeria Anhänger von Schiiten-Führer Ibrahim Zakzaky
Hoto: AFP/S. Adelakun

Wata kotu a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ce, ta bai wa jagoran Kungiyar 'yan Shi'a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky izinin zuwa kasar Indiya domin neman magani tare da mai dakinsa Zeena. Sai dai a yayin da hukumar tsaro ta farin kaya ta sanar da aiki da umurnin kotu bisa wasu sharruda da aka gindaya wa malamin, akwai batun lallai sai ya tafi da rakiyar jami’an tsaro, lamarin da yanzu haka ya haifar da cece-kuce a cikin kasar.