Dalilin tsamin huldar Amirka da Isra′ila | Labarai | DW | 25.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dalilin tsamin huldar Amirka da Isra'ila

Tsamin dangantaka tsakanin manyan abokan biyu, ta sake fitowa a fili bayan wani jawabin da shugaba Barack Obama ya yi. Musamman kan batun sasantawar Amirka da Iran da kuma kafa kasar Falasdinu.

Obama und Netanjahu Treffen Washington

Shugaban kasar ta Amirka ya ce "Ina da dalai na hulda ta da Firaminista Netanyahu, na sadu da shi fiye da ko wane shugaba tunda na hau mulki. Ina magana da shi a ko wane lokaci. Kun san cewa yana wakiltar kasarsa yadda ya so, haka ni ma. Matsalar bawai hulda tsakanin shugabannin ba, matsalar a bayyane ta ke, kuma mai cike da kalu bale ce. Mu mun yi imanin da kafa kasashe biyu na Israila da Falasdinu, kan cewa shi ne zai fi baiwa Isra'ila tsaro, shi ne kuma zai cika burin Falasdinawa da ma samar da zaman lafiya a yankin bakin daya. Wannan shi ne manufarmu kuma har gobe a kai muke, shi kuma Firaministan Netanyahu yana da hanya ta daban da yake son bi" Wannan dai shi ne kusan lokaci mafi muni a dangantakar Amirka da Isra'ila, kasashen da suka fi ko wadannen dasawa.