Dalilan kafa kanfanin dillacin labaran Faransa | Amsoshin takardunku | DW | 31.12.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Dalilan kafa kanfanin dillacin labaran Faransa

Mai sauraro na so ya san tun yaushe ne aka kafa kanfanin dillacin labaran Faransa AFP, da kuma yawan 'yan jarida da ke yi ma wannan kanfanin aiki?

Haɗarin 'yan jarida a lokacin farautar labarai a Iraƙi

Haɗarin 'yan jarida a lokacin farautar labarai a Iraƙi

Shi dai kanfanin dillacin labaran Faransa an kafashi ne a ranar 30 ga watan satumba ta shekarar 1944 wato shekaru 67 ke nan da suka gabata. Amma a ƙashin gaskiya kwana arba'in kafin rattaɓa hannu akan takardar kafa AFP, wasu tsageran 'yan jarida da ke fafitikar ƙwaco 'yanci a lokacin da ake tsaka da gwabza yaƙin duniya na biyu, suka yi nasarar kwace ginin da ke zama cibiyar kanfanin a yanzu a hannun abokan gaban ƙasar tasu ta faransa da kuma ƙawayenta, tare kuma da fara watsa rahoton AFP na farko daga tsakiyar birnin Paris a ranar 20 ga watan agusta ta 1944.

Bayan yaƙin duniya na biyu ne, AFP ya zama ɗaya daga cikin mahimman kafafe da ake dogaro da su wajen samun sahihan labarai kuma da ɗumi-ɗuminsu daga ko ta ina cikin duniya. Hasali ma dai, Kafar sadarwar ta ƙasar Faransa ce ta kasance ta farko daga cikin ruƙunin na ƙasashen yammacin duniya da ta sanar da mutuwar Joseph Stalline a ranar 6 ga watan maris na 1953.

Sauye-sauyen da aka samu daga bisani a kanfanin dillacin labaran Faransa, ya bayar da damar faɗaɗa ayyukansa baya ga labarai a rubuce, i zuwa na labarai cikin sauti da kuma hotuna na video, tare ma dai da fara watsawa labarai ta kafar sadarwa ta internet. A halin yanzu ma dai, AFP na watsa labaranta cikin harsuna shida na yammacin duniya ciki kuwa har da Faransanci, da turancin ingilishi, da Spaniyanci, da harshen portugiz, da larabci da kuma jamusanci.

Ma'aikata 935 da ke aikin dindindi a cibiyarta da ke birnin Paris kanfanin dillacin labaran faransa ya ƙunsa ciki kuwa har da 200 da ke suka ƙware a fannin ɗaukan hotuna da kuma ƙawatasu. Kazalika AFP na da wakilai aƙalla 2000 da suka fito daga ƙasashe 81 da kuma ke aiki a sassa daban daban na duniya.

Amince da majalisar dokokin Faransa ta yi a ranar 10 ga watan janairu ta 1957 da sauya matsayin AFP daga kanfani mallakar gwamanti i zuwa wanda ya ke da ƙwarya-ƙwaryar 'yanci, ya bai wa kanfanin dillacin labaran Faransa damar zama kanfani mai zaman kansa. Ko da shi ke gwamantin ƙasar ta Faransa ta na ci gaba da naɗa wakilanta a wasu mahimman guraben aiki a kanfanin, amma kuma ba ta ware ko da sisin kwabo ne ga AFP a matsayin tallafi. A daura da haka kanfanin na samun kuɗin shiga ne daga sayar da labaran da ta ke farautowa i zuwa gwamnatoci ciki kuwa har da ta Faransar, da ofisosghin jakadancin ƙasashe daban daban, da kuma uwa uba, kafofin watsa labarai ciki kuwa har da Deutsche Welle.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Yahouza sadissou