Dalilan da suke janyo karya darajar kudin kasa | Amsoshin takardunku | DW | 16.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Dalilan da suke janyo karya darajar kudin kasa

Akwai dalilan daban-daban da suke janyo kasa ta karya darajar kudinta, kamar abin da China ta yi kwanakin baya.

Abin da ya sa kasa take rage karfin kudi shi ne domin samun karin kudaden kasashen ketere wajen fitar da kayayyakin da aka sarrafa a kasar, kuma haka na daga cikin dalilan da China ta rage karfin kudin kasar cikin kwanakin baya.

Amma kasashe masu tasowa suka fuskantar matsala kan rage karfin kudi kamar kasashen Afirka, saboda ba sa fitar da kayayyakin da aka sarrafa, sai dai suna samar da kayayyakin da ake sarrafawa ga kasashe masu karfin tattalin arziki.