Dalilan da ke hana warware rikicin Siriya | Labarai | DW | 30.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dalilan da ke hana warware rikicin Siriya

Kimanin mutane 65 ne aka gano gawarwakinsu a yakin da ke ci gaba da wanzuwa a Siriya, yayinda kwamitin sulhun MDD ne ya gaza cimma matsaya akan rikicin.

Babban mai shiga tsakani na kasa da kasa a rikicin Siriya Lakhdar Brahimi ya yi gargadin cewar yakin da ke ci gaba da gudana a Siriya na ruguza kasar sannu a hankali, inda ya bukaci mambobin kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da su cimma matsaya guda wajen tilastawa bangarorin da ke rikicin su sami daidaito.

Akwai dai rarrabuwar kawuna a tsakanin kwamitin, inda Rasha da China ke hawan kujerar naki dangane da kudurorin da ke barazanar sanyawa Siriya takunkumi, wadanda kasashen Amirka da Faransa da kuma Birtaniya game da sauran kasashen yammacin duniya suka gabatar.

Barahimi ya ce kokarin shiga tsakanin da yake yi ba zai cimma wani buri ba muddin ba'a samu daidaiton ra'ayi a tsakanin kasashe mambobin kwamitin ba.

Furucin na sa ya zo ne jim kadan bayan gano gawarwakin akalla mutane 65 a birnin Aleppo da ke arewacin kasar ta Siriya, kamar yanda masu adawa suka sanar. Gawarwakin sun hada da na matasan da shekarunsu na haihuwa ya kama daga 20 zuwa 30 jibge a cikin kogin daya ratsa birnin na Aleppo. Dukkan gawarwakin kuma akwai alamar harbin bindiga sau daya tak da kuma rauni ko dai a kai ko kuma a wuya, inda gwamnatin Siriya da 'yan tawayen kasar ke zargin juna da tafka ta'asar.

Ya zuwa yanzu dai Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutane dubu 60 ne suka mutu yayin rikicin na Siriya na tsawon watanni 22.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu