1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dalilan da ke haddasa cutar Mageduwa

Abdourahamane Hassane
October 18, 2019

A cikin shirin za a ji cewa cutar Mageduwa cuta ce da ke kundule 'yan yatsu na kafa da ke bukatar watayawar iska don busar da 'yan yatsun wanda yawan samu damshin ruwa ke janyo yaduwar kwayoyin cuta.

https://p.dw.com/p/3RWuN
China Frau mit gebundenen Füßen
Hoto: picture-alliance/dpa/Imaginechina/He Huan

'Yan yatsu na kafa na bukatar watayawar iska don busar da tsakankaninsu wanda yawan samu damshin ruwa a tsakiyyar yatsun ke iya janyo yaduwar kwayoyin cuta da dama da suke haddasa ciwon Mageduwa. Farfesa Kabir Sabitu malami ne a Jami'are Ahmadu Bello da ke a Zariya ya bayyana cewa dole sai an dauki matakai idan har mutun na bukatar kaucewa fadawa cikin tarkon wannan ciyon.

Likitoci daga sassa dabam-daban sun kara yin bayyani a cikin shirin na "Lafiya Jari" adala dala a game da yadda cutar mageduwar ke faruwa da kuma ainahin yadda ta ke faruwa. 

Masu ciwon suga ma na iya samun wannan cutar ta mageduwa, saboda rashin kulawa da yaduwar cutar a jikinsu. Ku saurari shirin don jin karin bayani daga masana da kwarrun likitoci.