Dalibi ya kashe kansa bayan bude wuta a Jami′a | Labarai | DW | 24.01.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dalibi ya kashe kansa bayan bude wuta a Jami'a

Wani dan bindiga dadi ya kashe kansa bayan jikkata dalibai hudu da harsashi, lokacin da ya bude wuta yayin da suke daukar darasi a jami'ar Heidelberg da ke Kudu maso yammacin Jamus.

Kamfanin dillancin labaran Jamus dpa ya ruwaito mutuwar daya daga cikin daliban da suka jikkata sakamakon mummunar raunin harbin bindiga, sai dai 'yan sanda ba su tabbatar da labarin mutuwar dalibar ba a hukumance.

Binciken 'yan sanda na cewa harin ba shi da alaka da wata manufar siyasa ko addini ba, sai dai y'an sandan sun umarci mazauna kusa da jami'ar da su bi a hankali har sai an kammala bincike. Jami'ar Heidelberg yana kudu da birnin Frankfurt kuma yana da yawan mutane kusan 160,000, Jami'ar tana ɗaya daga cikin sanannun manyan makarantu a Jamus.