Dalibar Indiya da aka yi wa fyade ta mutu | Labarai | DW | 29.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dalibar Indiya da aka yi wa fyade ta mutu

Matashiyar kasar Indiya wadda fyaden da aka yi mata a motar safa a Delhi babban birnin kasar ya janyo zanga zanga ta mutu a kasar Singapore

Dalibar kasar Indiya wadda fyaden da aka yi mata a motar safa a Delhi babban birnin kasar ya janyo zanga zanga a fadin kasar ta cika a wani asibitin Singapore. 'Yar shekaru 23 da haihuwa, ta bar duniya sakamakon raunukan da ta samu yayin wannan fyaden. Wadanda su ka yi mata fyaden sun tika mata duka sannan su ka hurgo ta daga motar safa, tare da namijin da su ke tafiya. Zanga zangar da ta biyo bayan fyaden ta yi sanadiyar mutuwan dan sanda daya.

Firaministan kasar ta Indiya Mamnmohan Singh ya bayyana matukar bakin ciki da samun labarin mutuwar dalibar mai karatun aikin likita.Tuni gwamnatin kasar ta bayyana cafke bata garin da su ka aikata wannan danyen aiki, wadanda aka ce za su yaba wa aya zaki.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe