1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami'an tsaro sun mamaye hukumar zaben Kwango

Suleiman Babayo
January 9, 2019

Hukumar zaben Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango tana shirye-shiryen karshe na fadin sakamakon zaben shugaban kasa cikin yanayi na tararrabi da yuwuwar tashin hankali.

https://p.dw.com/p/3BFaq
Kongo hält mit zwei Jahren Verspätung historische Wahlen ab
Hoto: Reuters/O. Acland


'Yan sandan kwantar da tarzoma sun killace hukumar zaben Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango a wannan Laraba, inda ake sa ran bayyana sakamakon zaben shugaban kasa cikin tararrabi, bayan zargi tafka magudi. Rahotanni sun ce 'yan sanda cikin shirin ko-ta kwana su zagaye hukumar zaben da motoci masu sirke gami da masu dauke da ruwan zafi.

Jami'an hukumar zaben sun kwashe dare suna taro kuma ana sa ran kowanne lokaci za su bayyana sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar ranar 30 ga watan jiya na Disamba a wannan dirkekiyar kasa da ke yankin tsakiyar nahiyar Afirka, lamarin da ke zama karo na farko da za a mika mulki cikin kwanciyar hankali a kusan shekaru 60 da suka gabata a kasar ta Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, inda Shugaba Joseph Kabila da ya kwashe shekaru 18 kan madafun iko wa'adinsa ya kare tun shekaru biyu da suka gabata.

Akwai manyan 'yan takara uku da suka fata kan samun madafun ikon kasar da suka hada da Emmanuel Ramazani Shadary mai samun goyon bayan gwamnati, sai kuma hamshakin dan kasuwa Martin Fayulu da Felix Tshisekedi na babbar jam'iyyar adawa.