Dakile cin zarafin Zabiya a Afirka | Labarai | DW | 07.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakile cin zarafin Zabiya a Afirka

Majalisar dokokin Tarayyar Turai ta yi kira ga wasu kasashen nahiyar Afirka, musamman kasar Malawi da su kawo karshen cin zarafin da ake wa Zabiya a kasashensu.

Boniface Massah Albino Afrika Malawi

Wani Zabaya mai suna Boniface a kasar Malawi

A iri-irin wadan nan kasashe na Afirka da ke Kudu da Sahara, mutane na hallaka Zabiya tare da yin tsafi da wasu sassan jikinsu, yayin da wasu ma ke tona makarbarta inda aka rufe gawar ta Zabiya domin yin wasu sihirce-sihirce da a cewarsu zai sa su yi arziki nan take. Wannan matsala dai ta yi kamari a kasar ta Malawi, inda daga cikin Zabiyan kasar da aka kiyasta yawansu daga 7000 zuwa 10.000, jami'an tsaron 'yan sanda sun bada rahoton hare-hare da aka kai kan Zabiya 69, tare da kashe 18 daga cikinsu daga shekara ta 2014 kawo yanzu. Tun dai da jimawa kungiyar kare hakin dan Adam ta Amnesty International ta yi Allah wadai da wannan muguwar akida, inda aka kiyasta hare-hare da suka kai 448 kan Zabiya a cikin kasashe 25 na Afirka a shekara ta 2015 kawai.