Dakarun yaki da Boko Haram sun fara komawa Maiduguri | Labarai | DW | 08.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun yaki da Boko Haram sun fara komawa Maiduguri

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta fara mayar da shelkwatarta ta yaki da Boko Haram Maiduguri, a wani mataki na cika umurnin shugaba Buhari.

Lokacin jawabin rantsuwar kama aikinsa ne ya yi wannan sanarwar inda ya ce za a yi nasara kan masu tada kayar bayan ne kadai idan aka mayar da cibiyar yakin da su zuwa makarfafarsu.

Mai magana da yawun sojojin Sani Usman, ya fadawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, tawagar farko ta riga ta isa Maidugurin yanzu haka, sannan ya kara da cewa za a sake girka wata cibiyar a birnin Yola, fadar gwamnantin jihar Adamawa, inda a makon da ya gabata wani bam ya tashi a wata kasuwa har ma ya hallaka mutane 31.

A wata tattaunawa ta musamman da shugaba Buharin ya yi da takwaransa na Faransa Francois Hollande, a taron kasashen G7 masu samun ci-gaban masana'atu, ya bayyana cewa yana bukatar tallafin Faransar wajen samar da bayanan sirri domin gano gaskiyar dangantakar da kungiyar Boko Haram ke da shi da kungiyar IS, wadda ke da'awar kafa daular musulunci a Siriya da Iraki.