1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun wanzar da zaman lafiya sun kama aiki a Mali

July 1, 2013

Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya sun ƙaddamar da aikinsu a Mali da burin taimakwa ƙasar wajen gudanar da zaɓe.

https://p.dw.com/p/18zB0
UN peacekeepers mark the start of the 12,000-strong U.N. peacekeeping mission (MINUSMA) in Mali, in Bamako July 1, 2013. REUTERS/Adama Diarra (MALIP - Tags: POLITICS)
Hoto: Reuters

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙaddamar da ayyukan wanzar da zaman lafiyarta a ƙasar Mali a wannan litini, inda ta fara da shigar da dakarun ƙasashen yankin yammacin Afirka su sama da dubu shida a cikin rundunar nata.

Babban burin wannan runduna dai, zai kasance taimakawa gwamnatin riƙon ƙwaryar ƙasar wajen gudanar da zaɓen shugaban ƙasa mai tsabta, wanda ake sa ran yi ranar 28 ga wannan wata na Yuli.

Haka nan kuma ana sa ran sake faɗaɗa wannan runduna da dakaru sama da dubu 11 da ma 'yan sanda dubu ɗaya da ɗari hudu domin tabbatar da wannan buri.

Zuwan waɗannan dakaru dai, zai baiwa Faransa damar janye dakaru 4 500 daga cikin waɗanda ta tura a watan Janairu dan taimakawa wajen yaƙi da 'yan tawaye, kuma Faransar ta ce dakaru dubu guda kaɗai za ta bari su riƙa marawa dakarun Majalisar Dinkin Duniyar baya, daga yanzu zuwa ƙarshen shekara.

Kawo yanzu dai ƙasar ta Mali ta fara farfaɗowa daga rikicin da ya kusan durƙusar da ita, to sai dai hukumar zaɓen ƙasar na nuna shakku yiwuwar gudanar da zaɓen na ranar 28 ga watan Yuli sakamakon ƙalubalen shirye-shirye da na tsaro.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Zainab Mohammed Abubakar