Dakarun Siriya sun halaka sojin Turkiyya | Labarai | DW | 28.02.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Siriya sun halaka sojin Turkiyya

Kungiyar tsaro ta NATO na shirin zaman gaggawa kan kisan wasu sojojin Turkiyya da ake zargin rundunar gwamnatin Shugaba Bashar Al-Assad a yanki da ke hannun 'yan tawaye.

Sojojin kasar Turkiyya kimanin talatin da uku ne rahotannin ke cewa sun mutu a wani hari ta sama da ake zargin rundunar gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad ta kai kansu a yankin Idlib. Akwai wasu gwanmai da suka sami rauni daga artabun.

Ana dai ganin yawan sojojin da suka mutu sun zarce alkaluman da aka baiyana a yayin da Majalisar Dinkin Duniya da Amurka ke gargadin illolin da kazancewar rikicin yankin ka iya yi akan fararen hula da kokarin da ake yi na shawo kan rikicin da aka kwashi fiye da shekaru tara ana yi.

Kawo yanzu, gwamnatin Siriyan ba ta ce komai ba a game da harin da ake zarginta da kai wa, don sake karbe ikon yankin na Idlib, tungar karshe da ke hannun masu adawa da gwamnatinsa. Rundunar sojin Turkiyya ta kasance a Siriya don marawa 'yan tawayen baya.