1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mayakan IS 300 sun mika wuya a Siriya

Abdul-raheem Hassan
January 24, 2022

Dakarun Siriya na SDF, sun kai farmaki a wani bangare na gidan yarin da mayakan IS suka kwace a Arewa maso gabashin Siriya, tare da tilasta akalla mayaka 300 mika wuyan dole.

https://p.dw.com/p/461VB
Syrien Hassakeh IS Angriff auf Gefängnis
Hoto: AFP

Sojojin Syrian Democratic Forces (SDF), karkashin jagorancin mayakan Kurdawa na YPG sun ce har yanzu mayakan na ci gaba da yin katsalandan a wasu gine-gine, kuma an fara shirye-shiryen kakkabe sauran sansanonin da ke birnin Hasaka.

An kiyasta fursunoni 180 da 'yan tawae da jami'an tsaro 27 sun mutu, tun bayan da mayakan IS suka kai hari a gidan yarin a ranar Alhamis da zimmar kubutar da mambobinsu.