Dakarun NATO sun halaka a Afghanistan | Labarai | DW | 21.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun NATO sun halaka a Afghanistan

A wani sako da ya watsa ta kafar intanet a shafinsa na Twitter mai magana da yawun kungiyar ta Taliban ya ce sun halaka dakaru 19.

Wani dan kunar bakin wake dauke da bam a kan mashin dinsa ya afkawa wata tawagar sojin hadin gwiwa na Amirka da Afghanistan a kusa da sansanin sojin sama na Bagram da ke Afghanistan a ranar Litinin din nan, lamarin da ya yi sanadin kisan soja biyar da raunata wasu guda shida kamar yadda gwamnan lardin Bagram Abdul Shukur Qudusi ya bayyana.

A wani sako da ya watsa ta kafar intanet a shafinsa na Twitter mai magana da yawun kungiyar ta Taliban Zabihullah Mujahid ya ce su ne suka kai wannan hari da ya yi sanadi na dakarun soja 19 a cewarsa ya kuma raunata wasu da dama.

Shelkwatar tsaro ta dakarun kawanace na NATO ta tabbatar da afkuwar lamarin inda ta ce bayanan da ta samu wani abin hawa dauke da bam ya afkawa dakarunsu a kusa da filin tashin jiragen saman soji da ke a Bagram sai dai ta na ci gaba da bincike.