Dakarun Kwango sun ƙwace garin Kamango | Labarai | DW | 26.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Kwango sun ƙwace garin Kamango

Sojojin gwamnatin Kwango tare da tallafin sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya sun ƙwaci iko da garin wanda ke a yankin gabashin ƙasar kan iyaka da Yuganda.

A ranar Larba da ta wuce ' yan tawaye na ƙungiyar ADF-NALU suka karɓi iko da garin na Kamango. Masu aiko da rahotannin sun ce gwamnatin ta Kwango ta buƙaci taimakon MDD domin sake ƙwato garin.

Kuma majaliar ta tura jiragen sama masu saukar ungulu na Afirka ta Kudu da ke a ƙarƙashin ikon rundunar wanzar da zaman lafiya na majalisar, waɗanda suka rufa wa sojojin gwamnatin baya. A halin da ake ciki 'yan tawyen sun ja da baya zuwa garin Nobili wanda ke kan iyaka da Yuganda wanda kuma wata cibiya ce da ta tattara 'yan gudun hijira sama da dubu 150.

Ƙungiyar 'yan tawayen ta ADF NALU wacce ke a ƙarƙashin jagoranci Jamil Mukulu wani Kiristan da ya musulunta tun a shekara 2007. Amirka ta saka sunansa a cikin jerin 'yan ta'adda tun a shekaru 2001

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu