Dakarun Kurdawan Iraki sun kaddamar da wani farmaki kan ISIS | Labarai | DW | 17.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Kurdawan Iraki sun kaddamar da wani farmaki kan ISIS

Mayaka fiye da dubu 2 da 500 na Peshmerga ke cikin damarar kare yankunansu daga barazanar 'yan ta'adda na kungiyar ta Daular Islama.

Dakarun Kurdawan Iraki sun kaddamar da wani gagarumin farmaki da nufin sake kwace garin Sinjar na arewacin kasar daga hannun sojojin sa kai. Wannan farmakin dai wani bangare ne na kokarin tabbatar da tsaro a babbar hanyar da ke shiga kasar Siriya kai tsaye. Dakarun na Peshmerga da ke samun goyon bayan sojojin kawance da ke karkashin jagorancin Amirka, sun kutsa cikin garin da ya kasance hannun mayakan kungiyar IS tun cikin watan Agusta da ya gabata.

Kanal Zewaie da ke zama kwamandan bataliya ta hudu a ma'aikatar Peshmerga, ya ce yanzu haka akwai mayaka fiye da dubu 2 da 500 da ke cikin damarar kare yankunansu daga barazanar 'yan ta'adda. Yana da wahala a ga 'yan ISIL a kan tsaunin Sinjar. Kuma suna aiki tukuru don sake kwace yankin.