dakarun kungiyar Islam a sun kame wani sansani a wajen Mogadishu | Labarai | DW | 11.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

dakarun kungiyar Islam a sun kame wani sansani a wajen Mogadishu

Rahotanni daga kasar Somali,sunce fiye da yan kungiyar Islama 1,000 aka girke a sansanoni arewacin birnin Mogadishu.

Kodayake babu wani karin haske dangane da ko girke dakarun na islama yana wani bangare ne na kammala fatattakar yan tawaye da suka saura,ko kuma yunkuri ne na kai hari akan garin Jowhar da yan tawayen suke rike da shi.

Wadanda suka ganewa idonsu,sunce,mayakan na islama dauke da manyan makami sun isa sansanin soji na Hiilweyne mai tazarar kilomita 7 daga garin Balad wanda tunu suke rike da shi.