Dakarun Kenya sun farwa Al Shabab | Labarai | DW | 06.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Kenya sun farwa Al Shabab

Sojin Kenya sun kaida hare-haren boma-bomai a kan sansanoni biyu na mayakan Al Shabab da ke kasar Somaliya, karon farko bayan da kungiyar ta kaddamar da harin da ya halaka daliban kasar su 148.

Mayakan saman kasar Kenya sun kaddamar da hare-hare da boma-bomai a kan sansanoni biyu na mayakan Al Shabab da ke kasar Somaliya, karon farko bayan da kungiyar ta kaddamar da harin da ya halaka daliban jami'a 148 a gabashin Kenyan, a makon jiya.

Kamar dai yadda kamfanin labaran Reuters ya labarta, Jiragaen yakin Kenya sun yi luguden wutan ne kan Gondodowe da kuma Ismail da ke shiyar Gedo a Somaliyan.

Jamian sojin na Kenya, sun hakkake cewa daga yankin da suka yiwa barin wutan ne mayakan na Al shabab ke fitowa, suna kuma shiga kasar, suna mai bada misali da harin Garissa da mayakan suka farwa, da suka ce bai wuce tazarar Mil 120 ba da iyakan kasar.

Shugaba Uhuru Kenyatta na kasar Kenyan dai ya sha alwashin fuskantar Al shabab ba tare da sassauci ba, bayan harin na Garissa.