Dakarun kawance sun kaddamar da sabon farmaki a Afghanistan | Labarai | DW | 16.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun kawance sun kaddamar da sabon farmaki a Afghanistan

Dubun dubatan dakarun kawance dake karkashin jagorancin Amirka da sojojin Afghanistan sun kaddamar da wani sabon farmaki kan ´yan Taliban a wasu larduna biyar na Afghanistan. Wannan farmakin ya zo ne a daidai lokacin da dakarun da kungiyar tsaro ta NATO kewa jagoranci ciki har da sojojin Amirka dubu 2 da 500 ke ci gaba da fafatawa da ´yan Taliban a kudancin Afghanistan. Kawo yanzu an halaka daruruwan ´yan Taliban a cikin makoni 2 da fara wannan farmaki. A wani ci-gaban kuma Canada ta kara yawan dakarunta a Afghanistan da sojoji 200.