1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Jamus a Mali

February 19, 2013

Jamus ta amince da tura dakarun da zasu horas da sojojin yammacin Afirka tare da ma'aikatan ceto da likitoci dan tallafawa waɗanda suka yi rauni

https://p.dw.com/p/17h7h
Foto: DW/ Katrin Gänsler 19. Januar 2013, Bamako, Mali Bildbeschreibung: Malische Soldaten warten auf Einsatz und Ausbildung
Hoto: DW/ K. Gänsler

Jamus zata tura dakaru 330 zuwa ƙasar Mali, shawarar da majalisar zartarwar Jamus ta cimma ke nan. Zata tura dakaru 180 wadanda zasu horas da sojojin na yammacin Afirka, kana kuma da wasu 150 waɗanda zasu kula da harkar sufuri da kuma sanya mai a jiragen yaƙi.

Ranar litini ne ministocin harkokin wajen Turai suka cimma wannan matsaya inda suka amince su tura waɗanda zasu horas da dakarun Malin guda 450 da kuma wasu sojojin. Ana sa ran zasu shawarci dakarun na yammacin Afirka su kuma yi aiki tare wajen yaƙi da masu kaifin kishin addini. Jamus kuma zata sake tura wasu ƙwararru 40 waɗanda ke aikin ceto da kuma ƙarin wasu likitoci 40.

Idan aka amince da wani ƙuduri na biyu za'a samu goyon bayan kammala yaƙin da ake yi da 'yan tawayen na arewacin Mali. Ran Juma'a mai zuwa idan Allah ya kai mu ake sa ran majalisar dokoki na bundestag zata zauna da amincewa da ƙudurorin.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Yahouza Sadissou Madobi