Dakarun Isira′ila sun yi harbin gargadi cikin Siriya | Labarai | DW | 11.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Isira'ila sun yi harbin gargadi cikin Siriya

A karon farko dakarun kasar Isira'ila sun yi harbin gargadin cikin kasar Siriya.

Rundunar sojan Isira'ila ta bayyana yin harbi na gargadi, bayan da aka sake cilla mata rokoki kan tudden Golan, daga Siriya, wanda shi ne karo na farko tun bayan yakin tsakanin Isira'ila da kasashen Larabawa cikin shekarar 1973, da kasar ta Bani-Yahudu ta yi harbi cikin Siriya.

Wannan lamari ya fara barazanar fadada rikicin kasar ta Siriya, inda karo na biyu, cikin mako guda dakarun Isira'ila su ka fuskanci hari. Wannan daidai lokacin da zaman tankiya ke karuwa kan iyakar kasar ta Siriya da Turkiya.

A wani labarin 'yan adawan kasar ta Siriya, da su ka gudanar da taro a birnin Doha na kasar Qatar, karkashin matsin lamban kasashen duniya, sun amince da kulla kawance, domin kawar da shugaba Bashar al-Assad daga madafun iko.

Sabon kawance zai tabbatar da hada kai da tsirarun kabilu da addinai.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Zainab Mohammed Abubakar