Dakarun Iraki sun kwace garin Falluja | Labarai | DW | 17.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Iraki sun kwace garin Falluja

Dakarun Iraki sun samu nasarar kafa Tutar kasar a babban ginin gwamnati da ke garin Falluja, bayan kwace garin daga IS.

Dakarun Iraki sun kwace Falluja

Dakarun Iraki sun kwace Falluja

Wannan nasara dai na zuwa ne bayan kwashe tsahon kusan makwannin hudu da dakarun gwamnatin da kuma na sa kai suka yi suna gwabza fada da mayakan kungiyar ta'addan IS da ta kwace iko da garin. Dakarun Irakin sun shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa sun dan samu tirjiya daga wasu mayakan na IS da ke kauracewa garin a yayin da suka shiga Fallujan a wannan Jumma'a. Wannan dai shi ne gagarumin koma baya na baya-bayan nan da kungiyar ta IS ta samu, bayan tsahon shekaru biyu da ta ayyana kafa daular Islama a kasashen Irakin da Siriya, baya ga ayyana daular Islamar a Libiya da IS din ta yi a kwanakin baya.