Dakarun Iraki sun kammala fatattakar IS a Mosul | Labarai | DW | 09.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Iraki sun kammala fatattakar IS a Mosul

Firaministan kasar Iraki Haidar al-Abadi a wannan rana ta Lahadi ya isa birnin Mosul da ke zama wurin da ya yi saura a hannun mayakan IS kamar yadda gidan talabijin na kasar ya bayyana.

Babban kwamandan askarawan sojan kasar ya isa wanan birni inda ya taya dakarun da ke lugudan wuta kan mayakan na IS murna kamar yadda gidan talabijin din kasar ya nuna.

Jakadan Amirka cikin kawancen fatattakar ta IS Brett McGurk, ya tabbatar da zuwan na al-Abadi birnin na Mosul domin taya dakarun murna kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter.

Tun da fari dai jami'an tsaro sun fada wa kamfanin dillancin labaran Jamus na DPA cewa suna ci gaba da dannawa kan mayakan na IS a iya yankin da ya yi saura a hannunsu a wannan rana ta Lahadi a yammacin tsohon birnin na Mosul.