Dakarun Iraki na daf da kwato Mosul
June 30, 2017Talla
Rahotanni sun ce daruruwan mata da kananan yara ne suka tsirewa farmakin wannan Juma'ar, wasu daga cikinsu dauke da raunukan da mayakan na IS suka yi masu. Sai dai kwamandodjin sojin na Iraki na gargadin cewa ana iya fuskantar barazana daga 'yan IS din, ganin wasu daga cikinsu na cikin jama'a, kuma mai yiwuwa ne su afkawa mutane.
Wasu rahotannin ma na nunin janyewar IS din daga garuruwa 17 da ke lardin Aleppon kasar Syria, bayan kasancewar yankunan karkashin ikon kungiyar tsawon shekkaru hudu.