1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Indiya da Faransa na atisayen sojoji

Abdourahamane Hassane
January 25, 2019

Sojojin Faransa da na Indiya sun soma wani atisaye a cikin tekun Indiya, inda jiragen yaki na ruwa suka soma yin sintiri.

https://p.dw.com/p/3C9gW
Jacques Chirac in China Flagge
Hoto: AP

A shekarar bara ne dai Faransa da Indiya suka cimma wata yarjejeniya ta karfafa huldar tsaro a tsakaninsu. Kaso 25 cikin 100 na sufurin jiragen ruwa na duniya na bi ta tekun na Indiya, yayin da kasashen Turai ke da kaso 75 na yawan jiragen ruwan da ke ratsa tekun. Indiya wacce ke yin zaman doya da man ja tsakaninta da China sakamakon yadda take kara mamaye tekun Indiyar, na kallon atisayen a matsayin kandagarki.