dakarun gwamnatin Uganda sun fara janyewa daga arewacin ƙasar | Labarai | DW | 31.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

dakarun gwamnatin Uganda sun fara janyewa daga arewacin ƙasar

Gwamnatin Uganda ta bayyana janye dakarun ta daga arewancin ƙasar, kwana ɗaya bayan fara aiki da yarjejeniyar zaman lahia da ta cimma, tare da yan tawayen LRA.

Saidai kakakin rundunar gwamnati da ya bayyana labarin bai faɗi yawan sojojin da su ka janye ba.

Al´umomin Uganda, mussamman na yankunnan da rikicin ya shafa, sun shirya tafiyar jerin gwano cikin lumana, domin nuna farin ciki ,a game da massalaha da aka samu a cikin wannan rikici da ya ɗauki tsawan shekaru kussan 20 a na gwabzawa.