dakarun Gwamnatin Sudan sun kai sabin hare hare ga yan tawayen Darfur | Labarai | DW | 30.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

dakarun Gwamnatin Sudan sun kai sabin hare hare ga yan tawayen Darfur

Rahotani daga ƙasar Sudan, sun ce dakarun gwamnati tare da haɗin gwiwar yan Djandawid,sun kai sabin hare hare, ga yankin Darfur da ke fama da rikicin tawaye.

Rundunar ta kai wannan hari, kan wani saban haɗin gwiwar ƙungiyar yan tawaye, da su ka ƙauracewa yarjejeniyar zaman lahia, da ka rataba hannu kanta, a birnin Abuja na tarayya Nigeria.

Ɗaya daga shugabanin wannan ƙungiya Abou Bakr Hamid Al-Nour, ya sanar kamapanin dullancin labaru na Reuters cewar, a tsukin yan kwanaki 2 da su ka gabata, dakarun gwamnati sun kai samame, a yankunan Djabel Moun, da Koulkoul ,dake arewancin El Facher.

Annour, ya ƙara da cewa, dakarun gwamnati sun yi anfani da jiragen sama, masu saukar angulu guda 3, domin kai wannan hare hare, wanda a sakamakon su ɗaruruwan mutane su ka ƙaura daga gidajen su.

A wani labarin kuma, shugaban ƙasar Sudan Omar El Beshir, ya sake jaddada matsayin sa, na ƙin amincewa da karɓar dakaru shiga tsakani na majalisar Ɗinkin Dunia a yankin Darfur.

Al Beshir ya yi barazar cewa,muddun wannan dakaru su ka sa kafa a yankin Darfur ko shaka babau zai zama ajjalin.

A cikin jawabin da ya gabatar, ya ce idan Majalisar Ɗinkin Dunia na buƙatar bada agaji, ga al´ummomin Darfur mi ta ke jira ta taimakawa Labanon da ke fama da hare hare Isra´ila.