Dakarun gwamnatin Iraƙi sun ƙwace iko da garin Baiji | Labarai | DW | 14.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun gwamnatin Iraƙi sun ƙwace iko da garin Baiji

Dakarun sun karɓe iko da garin mai matatar man fetir mafi girma da ke a yankin arewacinn kasar bayan sun kwashe kusan makonnin huɗu suna gwabza ƙazamin fada da Ƙungiyar IS.

Masu aiko da rahotannin sun ce sake karɓe iko da birni na Baiji da ke a arewacin bagadaza. Zai ƙara ƙwarin gwiwa wa dakarun gwamnatin wajen ƙarfafa tsaro a kan matatar man fetir ɗin da mayaƙan IS suka ƙwace a cikin watan Yunin da ya gabata.

Wannan yunƙurin dai na sojojin gwamnatin na iraki na zaman wata babbar nasara da suka samu a kan masu jihadin tun lokacin da aka fara yin faɗan.