1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Faransa sun kwace garin Gao

January 26, 2013

Dakarun sojan Faransa sun kwace iko da garin Gao na arewacin Mali bayan kwashe kwanaki 16 ana artabun sake fatattakar 'yan tawayen daga arewacin kasar.

https://p.dw.com/p/17SAn
French soldiers, who prepare for their departure for Mali, walk past armoured vehicles during a visit of the French Defence Minister at the military base of Miramas, southern France, January 25, 2013. REUTERS/Jean-Paul Pelissier (FRANCE - Tags: MILITARY POLITICS)
Hoto: Reuters

Dakarun sojan Faransa sun kwace iko da garin Gao na arewacin Mali da kuma gadar Wabary mai muhimmanci, cikin kwanaki 16 da sojojin su ka kwashe su na luguden wuta kan 'yan tawaye da su ka mamaye yankin arewacin kasar ta Mali.

Ma'aikatar tsaron Faransa ta ce dakarun na ci gaba da samun galaba na kutsawa cikin arewaci tare da kwace yankuna daga hannun 'yan tawaye. Inda yanzu haka sojojin kasar ta Faransa kimanin 2,500 ke kasar ta Mali.

A wani labarin majiyoyin tsaron Mali sun ce dakarun sojan Jamhuriyar Nijar da na kasar Chadi sun kutsa cikin kasar ta Mali daga daya bangaren domin ritsawa da 'yan tawayen. 'Yan tawayen kasar ta Mali na ci gaba da faduwa babu nauyi tun bayan da dakarun Faransa su ka kaddamar da hari.

Firaministan Faransa Jean-Marc Ayrault ya ce nan gaba kadan dakarun kasar za su kutsa cikin garin Timbuktu domin kwacewa daga hannun 'yan tawaye da ke da alaka da kungiyar al-Qaeda.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh