Dakarun Faransa sun kai hari a kan AQMI | Labarai | DW | 10.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Faransa sun kai hari a kan AQMI

Fadar gwamnatin Faransa ta sanar da cewar dakarunta sun kai hare-hare a kan wani ayarin na mayaƙan AQMI a kan iyakar Libiya da Mali.

A cikin wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta bayyana, ta ce an ƙaddamar da hare-haren ne,tare da haɗin gwiwar gwamnatin Nijar a kan jerin gwanon ƙungiyar da ke kan hanyar zuwa Mali daga Libiya.

Kuma hare-haren sun yi sanadiyyar lalata makamai da tankoki yaƙi da masu kishin addini ke ɗauke da su zuwa Mali.Sannan an kama wasu da dama daga cikinsu tare kuma da sauran manyan makamai.