Dakarun al-Shabab sun hallaka a harin kunar bakin wake | Labarai | DW | 21.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun al-Shabab sun hallaka a harin kunar bakin wake

Da fari al-Shabab ta ce ita ke da hannu wajen kai wannan harin da ta yi ikirarin cewa ya yi sanadin kashe mutane da dama a Somaliya.

An ji karar wasu ababan fashewa sannan karar barin wuta na bindigogi a ranar Lahadin nan a tsakiyar baban birnin Mogadishu na kasar Somaliya.

Lamarin da ya faru a kusa da cibiyar bada horo ga jami'an leken asiri ta kasa kamar yadda wadanda su ka sheda lamarin su ka tabbatar wa da kamfanin dillancin labaran Reuters.

A cewar ma'aikatar harkokin cikin gidan Somaliya cikin dakarun na al-Shabab uku da su ka kai harin sun halaka, amma babu wanda harin ya ritsa da shi daga bangaren sojojin gwamnati.

Tuni dai kungiyar mayakan sakai ta al-Shabab ta ce ita ke da hannu wajen kai wannan harin da ya yi sanadin kisan mutane da dama a cewarta.