Dakaru Saudiyya sun kashe 'yan Huthi 126 | Labarai | DW | 05.11.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakaru Saudiyya sun kashe 'yan Huthi 126

A samamen da aka kai cikin sa'o'i 24 a yankin Marib na Yemen inda gwamnatin ke da karfin fada a ji, dakarun kawancen Saudiyya sun kashe kimanin 'yan tawayen Huthi 126.

Kawancen da ke marawa gwamnatin Yemen da kasashen duniya suka amince da ita ta bayar da rahoton shafe tsawon wata guda tana kai hare-hare a kusan kullum kan 'yan tawayen Huthi da ke samun goyon bayan Iran, tare da ikirarin gagarumar asara. Dakarun kawancen sun kuma ce sun lalata motoci 16 na mayakan.

Tun dai a watan Fabarairun da ya gabata ne dai 'yan tawayen Huthi suka fara yunkurin kwace ikon birnin na Marib, sai dai bayan numfasawa; sun sake dasa dambar kwace ikon yankin a watan Satumbar da ya gabata. 

Yankin na Marib da ke zama babban birnin yankin mai arzikin mai ya kasance yanki na karshe a arewacin kasar da ke karkashin ikon gwamnati. A shekarar 2014 ne yakin basasa ya barke a kasar ta Yemen lokacin da 'yan tawayen suka kwace ikon babban birnin kasar Sanaa, lamarin da ya tilasta wa dakarun da Saudiya ke jagoranta marawa gwamnatin kasar baya.

Dubban mutane ne suka rasa rayukansu yayin da miliyoyi suka rasa matsugannsu.