Dakar: Shari′a kan zargin ta′addanci ta kammala | Labarai | DW | 01.06.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakar: Shari'a kan zargin ta'addanci ta kammala

Wata kotun ta musamman da ke hukunta manyan laifuka a birnin Dakar na kasar Senegal, ta kammala shari'ar wasu mutane 29 da ake zargi da ayyukan ta'addanci, amma kuma sakamako sai a ranar 19 ga watan Yuli.

Shari'ar da aka yi ta cikin tsauraran matakai na tsaro, ta soma ne tun daga ranar tara ga watan Afrilu da ya gabata bayan da aka sha dage ta tun daga watan Disamba na karshen shekarar da ta gabata, ta kasance shari'a mafi girma da aka yi kan harkokin ta'addanci da yawan wadanda ake zargin ya kai wannan adadi na mutun 29 kaman yadda Shugaban kotun Samba Kâne ya sanar.

Lauyoyin da ke kare wadanda ake tuhumar sun kammala bayanansu a gaban kotun, inda suka nemi da a sallami mutanen 29 cikinsu har da mata uku da ake tuhuma da ayyukan ta'addanci da suka hada da barazanar kai hari, gama baki da 'yan ta'adda, samar da kudi ga 'yan ta'adda, ko kuma halasta kudadan haramu.