Daidaituwar al′amura a Afrika ta Tsakiya | Siyasa | DW | 05.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Daidaituwar al'amura a Afrika ta Tsakiya

Harkoki sun fara komawa dai dai a kasuwanni da ma'aikatu a Jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya. Sai dai har yanzu wasu bankunan Kasar basu fara aiki ba.

Wasu mutane sunyi cirko- cirko a gaban babban Bankin Kasar Jamhuriyar Afrika Tsakiya dake bukatar fitar da kudadensu, saidai kuma Bankin ya kasance a rufe. Wani mazaunin garin na Bangui da ya zo Bankin domin fitar da wasu kudadensa yace.


"An rufe Bankin sam, sannan ga masu bukatar fitar da kudi nan sun yi cincinrindo ba tare da sun cimma bukata ba. Yanzu ma na hadu da shugabar Bankin inda ta shaida mana an yi kwasar ganima har ba iyaka a Bankin don haka ko zasu bude ba dai yau ba."


kamar yadda yake a wannan Bankin haka sauran dake cikin Birnin da ma na kauyuka suke fuskantar wannan matsalar ta kwasar ganima abun da ke nuni da cewa har yanzu akwai sauran jan aiki a gaba. Kazalika a fannin agaji ta la'akari da halin da mutane ke ciki nan ma akwai tarin matsaloli ko dayake a wani asibitin dake tsakiyar Birnin, babban Jami'in kiwon lafiya ya ce an samu dawo musu da ruwa da kuma wutar lantarki ta yadda zasu iya aiki cikin tsanaki.

die Stadt Bossembélé (im West) - mit einem Plakat gegen AIDS für mein Land kämpfe ich gegen AIDS (also: dieses Bild ist nicht besonders für die Wahl, aber vielleicht falls jemand einen Artikel über AIDS in Afrika schreibt) Foto DW/Cécile Leclerc 06/2010


"Bayan na yi kiran neman taimako a gidan rediyo wasu da dama sun kawo mana dauki sannan kuma ita ma Gwamnatin ta dau matakan bada ruwa da wutar lantarki a Asibitin. A yanzu dai kusan kashi 80 zuwa 90 na ma'aikatanmu sun dawo bakin aikinsu."
A hannu guda kuma tsohon Shugaban Kasar Francois Bozize ya zargi makwabciyarsa Kasar Chadi da laifin taimakawa 'yantawayen na Seleka da suka jagoranci kifar da Gwamnatinsa, Zargin da wani Jami'i a Kungiyar sanya Idanu kan rikice rikice ta Kasa da Kasa Thiery Vircoulan ke cewa akwai yiwuwar hakan.

"Ina ga akwai shaidu da dama dake nuna hakan, saboda daga cikin mayakan "yan tawayen akwai 'yan Kasar Chadi dama 'yan Kasar Sudan, saidai kuma abin da ba'a kammala tantancewa ba shine, shin wa suke taimakawa? suna yakine domin kare kasar Chadi, ko kuwa domin taimakwa 'yan tawayen ne ko kuma kawai irin mutanen nan ne da ake samu akan iyakokin Chadi da kuma Sudan? Har yanzu wadannan tambayoyi ne da ba'a gano amsarsu ba".

An dai gudanar da wani taro na Kasashen yankin Afrika ta Tsakiya a Ndjamena babban Birnin Kasar ta Chadi, inda bayan kammala taron Shugaban Kasar Chadin Idris Deby ya shaidawa manema labarai cewa ba zasu amince da Gwamnatin kamakarya da 'yantawayen Seleka suka kafa a Afrika ta Tsakiya ba, tare kuma da bayyana cewa dolene a kafa Gwamnatin rikon kwarya da zata shirya zabe cikin watanni 18 a Kasar, batun da Shugaban Gwamnatin 'yantawayen ta Seleka Micheal Djitodia ya bayyana amincewarsa da shi.


New Central African Republic leader Michel Djotodia speaks on Republic Plaza in Bangui on March 30, 2013 . The Central African Republic's new strongman Michel Djotodia vowed Saturday not to contest 2016 polls and hand over power at the end of the three-year transition he declared after his coup a week ago. AFP PHOTO / SIA KAMBOU (Photo credit should read SIA KAMBOU/AFP/Getty Images)

Michel Djotodia

A wani cigaban kuma Shugaban Kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya bayyana cewa zai janye Sojojin Kasar sa daga Jamhuriyar Afrika ta Tsakiyar biyo bayan mutuwar Sojojin kasar 13 yayin juyin mulkin da akayi, batun da yayi sanadiyyar samun matsin lamba da shugaba Zuman yayi daga bangaren Jamiyyun adawar kasar.
Zuma yace zai janye sojojinne kasancewar aikin da aka kaisu suyi ya kare tunda 'yantawaye sun riga da sun karbe iko da kasar kuma an tura sojojinne domin su bada horo ga sojojin Gwamnati karkashin Francois Bozize da aka yiwa juyin mulki.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe

Sauti da bidiyo akan labarin