1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Daidaito kan kundin tsarin mulkin a Sudan

Abdul-raheem Hassan
August 3, 2019

Kungiyar Tarayyar Afirka AU ta tabbatar cewa majalisar mulkin kasar Sudan da babbar jam'iyyar hadaka sun cimma yarjejeniyar ayyana sabuwar gwamnatin rikon kwarya kan kundin tsarin mulki.

https://p.dw.com/p/3NHCN
Unruhen im Sudan | Demonstration
Hoto: picture-alliance/Photoshot

An cimma wannan yarjejeniya ne bayan da yunkurin hakan ya cutura sau da dama saboda takun saka tsakanin bangarorin biyu kan shugabanci tun bayan hambara da tsohon Shugaban kasar Omar al-Bashir a watan Afirilun 2019. Fararen hula da dama sun mutu a jerin zanga-zangar neman iko da gwamnati.

Ana sa ran shugabannin bangarorin biyu za su kaddamar da bikin sa hannu kan sabuwar yarjejeniya da zai samar da gwamnatin hadakar soji da farar hula, da za su shugabanci kasar na tsawon shekaru kamin sabon zabe.