Dage zaben Najeriya, ina aka dosa? | Siyasa | DW | 19.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Dage zaben Najeriya, ina aka dosa?

Bayan da aka dage zabukan Tarayyar Najeriya, kungiyoyin fararen hula na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da dalilan dage zabukan.

Batun dage zabukan na Tarayyar Najeriya da zummar yaki da ta'addanci cikin makwanni shida dai, ya sanya shakku a zukatan mafiya akasarin al'ummar kasar, ta yadda wasu ke da ra'ayin cewa jami'an tsaron kasar na zaman 'yan amshin shatan gwamnati ne kawai. Da dama dai na ganin cewa an dage zabukan na Najeriya ne da wata manufa ta daban bawai domin yakar kungiyar Boko Haram da hukumar tsaron Najeriyar ta ambata ba. Dakta Abubakar Mu'azu malami ne a tsangayar nazarin harkokin aikin jarida a jami'ar Maiduguri, kuma mamba a kungiyar Borno Coalation for Democracy Development da kuma cibiyar tabbatar da zaman lafiya ta Center for Peace and Diplomatic Development Studies na daya daga cikin wadanda ke da irin wannan ra'ayi.

Nigeria Wahlen 2011 Bild 2

Ba dole ne a yi zabuka a ko wanne sashe ba

Dakta Mu'azu ya kara da cewa da yawa daga 'yan Najeriya basu ji dadin dage zabukan ba. Ko da yake wasu na ganin dage zabukan ka'iya baiwa jami'an tsaron damar kawar da kungiyar Boko Haram, wanda hakan zai iya bada damar yin zabuka a yankunan da kungiyar ke iko da su, sai dai Dakta Mu'azu ya ce ai ba wajibi bane a ce sai an yi zabukan a kowanne yanki, inda ya bayar da misali da kasashen Afghanistan da Iraqi da dukkaninsu ke cikin yaki kuma suka gudanar da zabukan.

Shi kuwa a nasa bangaren kwamared Kabiru Sa'idu Dakata na cibiyar bunkasa fasahar sadarwa wato Center for Information Technology and Development CITAD da ke jihar Kano a Tarayar Najeriyar, daya daga cikin kungiyoyi da ke horas da al'umma musaman a yankunan karkara kan muhimmancin zabe da kuma gudanar da shi cikin kwanciyar hankali, ya ce hakan ya kawo shakku sosai dangane da sahihancin dalilan dage zabukan.

Dage zabukan ya shafi mutane

A cewarsa koda yake basu ji dadin dage zabukan ba hakan ba zai sanya su yi kasa a gwiwa wajen ci gaba da wayar da kan al'ummar ba. Itama a nata bangaren Barrister Aisha Ado Abdullahi wata lauya mai zaman kanta a jihar Kano kuma shugabar kungiyar yaki da cin zarafin yara kanana ta Coalation Against Rape and Violance dake jihar ta Kano ta ce dage zaben ya shafi mutane da dama. Barister Ado Abdullahi ta kuma bukaci 'yan Najeriya da su kwantar da hankulansu kada kuma su yi duk wani abu da ke kama da na tayar da tarzoma.

DW.COM