1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwango: dage zabe ya bar baya da kura

Yusuf Bala Nayaya MAB
December 27, 2018

Mazauna yankin Goma da arewacin Kivu na Kwango sun nuna fushinsu dangane da dage zaben gama gari daga ranar 30 ga watan Disamba zuwa watan Maris saboda matsalolin da yankunan ke fama da su.

https://p.dw.com/p/3AglV
Kongo Beni | Protest & Demonstration
Hoto: Getty Images/AFP/A. Huguet

Dagewar da aka yi a yankunan na Beni da Butembo a arewacin Kivu da Yumbi a yankin Kudu maso Yamma ba za ta shafi kafatanin zaben shugaban kasa da 'yan majalisa ba. An dai dage zaben har sau uku wanda ake fatan zai kawo karshen gwamnatin Shugaba Joseph Kabila a wannan kasa mai albarkatun karkashin kasa da ta dauki tsawon shekaru 18 a yanayi na tashe-tashen hankula.

 Gédéon Sépéngwa, shugaban rukunin matasa a jam'iyyar UDPS a yankin na arewacin Kivu ya ce: "Ya zama dole a yi zabe a dukkanin fadin wannan kasa a lokaci guda. Abin dama mun rigaya mun fadi cewa Shugaba Kabila ba shi da niyyar sauka daga mulki, haka ita ma hukumar da ke shirya zabe mai zamanta CENI ba su shirya ba kan wannan zabe."

Za a bayyana sakamakon zaben shugaban kasar Kwangon a ranar 15 ga watan Janairu kana a rantsar da shugaban kasa 18 ga watan na Janairu kamar yadda hukumar CENI ta nunar. Sai dai ba ta yi bayani ba kan yadda za a yi da sakamakon zaben yankunan masu fama da matsaloli ba.

DR Kongo | Präsidentschaftswahlen 2018 - Wahlcomputer
Zabe ba zai gudana a Kivu ba duk da na'ura da Ceni ta tanadaHoto: picture-alliance/ZUMAPRESS

  A cewar Sépéngwa na matasan jam'iyyar UDPS abu ne da ya nuna cewa ana wasa da hankalinsu: "Wannan abu ne da ke bamu ciwon kai, mun gaji da abin da ake mana ba za mu ci gaba da lamunta ba. Abin da muke muradi shi ne, za mu hada gangami da zai jawo sanadi na tafiya da kujerar Kabila, saboda muddin Kabila nan to tsammaninmu na zabe ko mafarkinmu ba zai taba zama gaskiya ba."

Hukumar zaben kasar ta Kwango dai na kafa dalilai na matsalar 'yan ta'adda a arewacin Kivu haka kuma akwai matsalar cutar Ebola a yankunan Beni da Butembo. A cewar George Yalala, malamin makaranta a yankin Bukavu matakin dage zabe bisa kafa wadannan hujjoji ba za su taba gamsar da su ba.

Ya ce: " wannan mataki da hukumar zabe ta CENI ta dauka tamkar kunar bakin wake ne, mataki ne maras tushe. Mun sani cewa kasancewar akwai cutar Ebola da aka kakaba a yankin Butembo-Béni abu ne da ba za a taba kafa hujja da shi ba a ce an dage zabe."

Mutane sama da miliyan daya da dubu dari biyu ne suka yi rijistar zabe a yankunan da ake  fama da matsaloli dalilan dage zabe, yayin da a rijistar zabe a fadin kasar ake da mutane miliyan 44.