1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dage taron sulhunda Uganda da mako guda

Zainab A MohammadJuly 24, 2006
https://p.dw.com/p/Bu66

An sake dage zaman tattaunawar sulhunta gwamnatin Uganda da yan tawayen kasarna tsawon mako guda,tattaunawar dake da nufin gano bakin zaren warware rigingimu na tsawon kusan shekaru 20.

Wannan zaman sulhu da aka kaddamar a ranar 14 ga watan yunin daya gabata agarin Jubadake kudancin Sudan dai, nada nufin warware rikicin arewacin Ugandan ,wanda aka dauki shekaru 19,ana gwabzawa tsakanin dakarun gwamnatin da yan tawayen,fadan da ya kashe dubban mutane,ayayinda sama da million biyu,suka rasa matsugunnensu.Kakakin kungiyar yan tawaye na LRA na Ugandan,Obonyo Olweny ya fadawa manema labaru cewa an dage taron ne saboda gudanar da wasu bincike da tuntuba.