1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Da sauran aiki dangane da karin albashi a Najeriya

September 21, 2018

Kasa da mako guda da cikar wa’adin kungiyoyin kwadagon Najeriya kan albashi, har yanzu tana kasa tana dabo tsakanin mahukunta da kuma kungiyoyin da ke barazanar ajiye aiki.

https://p.dw.com/p/35J7q
1. Mai in Nigeria
Hoto: DW

In dai har akwai abu guda daya da ya yi nasarar hade daukacin kugiyoyin kwadagon  Najeriya guda uku na TUC da UCL da kuma NLC, ba zai wuce batun sabon albashin ma’aikata a kasar ba.

Sannu a hankali dai wa’adin karshen Satumba na kara karatowa kuma sannu a hankali gwamnatin kasar tana fadin har yanzu da sauran aiki. A karshen watan Nuwambar bara ne dai Abujar ta yi nasarar kafa kwamitin da take fatan ya ba ta shawara kan harkar albashin kuma Misis Amma Pepple, tsohuwar shugabar ma’aikatan Najeriya kuma  shugabar kwamitin da daukacin ma’aikatan kasar ke da fatan sauya makomar rayuwarsu a yanzu.

Nigeria Abuja - Sicherheitskräfte vor National Assembly
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Ta ce ‘’muna  aiki tukuru, kuma ina da imanin komai na tafiya dai dai, kuma muna jiran yawan adadi daga gwamnatin Tarrayar Najeriya, don ka sani dole ne mu tuntubi gwamnatocin jihohi, muna son adadi domin sanin abin da za mu saka a cikin rahotonmu. Za mu kira taro kwanannan, ina sa ran rahotonmu zai kamalla kafin karshen wannan wata.”

Ma’aikatan Najeriya dai na neman adadin da ya kai Naira dubu 56 ne a matsayin mafi karancin albashin, a yayin kuma da majiyoyi na gwamnatin kasar ke cewar ba za ta iya biyan abin da ya haura Naira dubu 25 ba, in har ana bukatar iya kaiwa  ga biyan daukacin ma’aikatan Tarrayar da kuma jihohi.

Ko yaya take shirin kayawa dai na iya kai wa ga kare makon goben na nufin tsayar da harkoki na gwamnatin kasar dama kila gurgunta daukacin harkokin tattallin arziki, a fadar Comrade Kabir Nasir, kakakin kungiyar kwadago ULC. To sai dai kuma in har tana shirin baki da duhu a tunanin ‘yan aikin a fadar Dr. Chris Ngige, ministan kwadagon Tarrayar Najeriyar, ai gwamnatin kasar ta cancanci yabo ko bayan kokari na ingancin albashin.

Abin jira a gani dai na zaman iya girma na murmushin ma’aikatan da ke zaman na kan gaba a cikin mafiya samun albashi mara tsoka a daukacin nahiyar Afirka.