Cyprus ta kafa asusun magance matsalar tattalin arzikinta | Labarai | DW | 21.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cyprus ta kafa asusun magance matsalar tattalin arzikinta

Shugabannin tsibirin Cyprus sun dukufa wajen ganin kasar ta tara yawan kudaden da take bukata kafinsamun tallafai daga tarayyar Turai EU da kuma asusun IMF.

Jam'iyun siyasa a tsibirin Cyprus mai fama da matsalolin tattali arziki, sun amince da kafa abin da suka kira "Asusun Zumunta" da nufin ceto kasar daga talaucewa. Shugaba Nikos Anastasiades ya ba da sanarwar kafa asusun bayan wani taro da shugabannin jam'iyun siyasa a birnin Nikosia. Sai dai har yanzu shugabannin kasar na tattaunawa game da abubuwan da sabon shirin zai kunsa. Amma rahotanni sun ce za a samar wa asusun kudi ne daga kadarorin coci, kudaden fansho da sauran hukumomin lamuni na kasa domin tara euro mliyan dubu 4.8 da kasar ke bukata. Shi ma babban bankin kasar zai taimaka da ajiyarsa ta zinare, yayin da sauran kudaden kuma za a tara ne daga hajarin da za a tilasta wa masu ajiya a bankuna da kudadensu suka haura euri dubu 100 biya. Dole kasar ta Cyprus ta samar da kudi euro miliyan dubu 5.8 da kanta, kafin ta samu tallafi daga tarayyar Turai da kuma asusun ba da lamuni na duniya wato IMF.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar