Cutar Ebola tana ci gaba da hallaka mutane a Guinea | Labarai | DW | 26.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cutar Ebola tana ci gaba da hallaka mutane a Guinea

An sake samun wadanda suka mutu bisa cutar Ebola a kasar Guinea

Karin mutane biyu sun mutu sakamakon kamuwa da cutar Ebola a kasar Guinea da ke yankin yammacin Afirka, abin da ya kawo adadin wadanda cutar ta hallaka zuwa 61.

Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa cutar mai sauri kisa ta shiga kasar Liberiya wadda ke makwabtaka da kasar ta Guinea Conakry. Akwai mutane 11 da ake kyautata zaton cutar ta kama a Liberiya, kuma biyar daga ciki sun mutu a wannan makon. Cutar ta Ebola ta barke a kasar Guinea kusa da iyaka da Liberiya, kawo yanzu ma'aikatar kula da kiwon lafiya ta kasar Guinea ta yi rijistan kimanin mutane 100 da suka kamu da chutar.

Kungiyar ba da agaji ta likitoci na gari na kowa da tura da karin jami'ai da kayan aiki domin dakile cutar ta Ebola mai haddasa mashasshara da janyo mutuwa nan take.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal