1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harkar canjin kudaden ketare ta ja da baya a Najeriya

February 26, 2020

Bullar cutar Coronavirus ko COVID-19 a wasu kasashen duniya na barazanar durkusar da kasuwar 'yan canjin kudaden ketare a Najeriya.

https://p.dw.com/p/3YTv8
Dollar Real Wechselkurs Symbolbild Währung USA Brasilien
Hoto: Getty Images/AFP/V. Almeida

A sakamakon bullar cutar Coronavirus kasuwar 'yan canjin kudaden musaya na ketare kama Dalar Amirka da sauran kudaden kasashen ketare tsayawa ca, saboda rashin matafiya da sauran 'yan kasuwa 'yan Najeriya da ke zuwa sayan kayayyaki kasashen da cutar ta bulla. Hakan ya sanya masu sana'ar canji kokawa bisa ga wannan cutar da ke neman gurgunta harkokin kasuwancinsu.

Mallam Alasan Mohammed daya ne daga cikin 'yan kasuwar Kaduna da ke yin sana'ar canjn kudi wanda ya bayyana yadda bullar wannan cuta ta dakatar da harkokin cinikayyar kudaden kasashen ketare a Najeriya.

Ya ce dukkanin masu sayan kudaden wajen sun ja da baya.

"Kwastomominmu da ke zuwa sayan kudaden kasar Sin da masu zuwa Dubai sun daina zuwa saboda fargabar kamuwa da cutar, kuma wannan lamari ya jefa mu cikin wani hali na rashin samun kudade don kula da iyalenmu."

Nigeria Symbolbild Korruption
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Kaduna da ke zama cibiyar daukacin jihohin arewacin Najeriya, ita ce jihar da aka fi samun kudaden kasar Si wato Chaina da na wasu kasashen Turai a sauwake, saboda irin yawan 'yan kasuwa da 'yan Boko da ke tafiye-tafiye zuwa wadannan kasashe.

Najeriya dai ta kasance daya daga cikin kasashen duniya da ke dogaro da kayayyakin kasar Sin, to ko yaya bullar wannan cutar ta shafi manyan 'yan kasuwar Najeriya da ke zuwa kasar Sin? Alhaji Mohammed Dan Auta shi ne kakakin kungiyar 'yan kasuwar jihar Kaduna da ke ya ce:

"Duk duniya babu kasar da ta fi amfani da kayayakin kasar Sin kamar Najeriya a saboda haka za a fuskanci karancin kayayyaki. A sanadiyyar wannan cuta 'yan kasuwar Najeriya suna dari-darin zuwa kasashen da aka samu labarin bullar cutar."

Kwararru a bangaren kiwon lafiya sun shawarci matafiya daga Najeriya zuwa kasashen ketare wajen rigakafin kamuwa da cutar.