Cudeni in cudeka tsakanin Sudan biyu | Labarai | DW | 22.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cudeni in cudeka tsakanin Sudan biyu

Shugabannin Sudan da Sudan ta kudu sun shan alwashin ci-gaba da harkokinsu na man fetur tare da warware rikicin kan iya da ke tsakaninsu cikin ruwan sanyi.

Shugaban Sudan da kuma takwaran aikinsa na Sudan ta Kudu sun kudiri aniyar yin aiki kafada da kafada da nufin karfafa harkar jigilar man fetur da ke tsakaninsu. Shugabannin biyu sun bayyana haka ne a Juba a lokacin wata ziyara da ke zama ta biyu da shugaba Omar Hassan al Bashir ya kai tun bayan da Sudan ta Kudu ta samu 'yancin cin gashin kanta.

Kasashe biyu da ke gaba da juna sun ta samu matsala game da jigilar man fetur da Sudan ta Kudu ta mallaka sakamakon rikicin kan iyaka da ke tsakaninsu da ke kuma rashin jituwa kan kaso da ya kamata a ware wa Sudan a matsayin kudin komisho. Ita dai Sudan ta Kudan ta na amfani ne da bututun kasar Sudan wajen jigilar manta zuwa kasuwannin duniya. yayin da a daya hannun kuma a watan satumba da ya wuce al'umar Sudan suka shafe kwanaki suna gudanar da zanga zanga bayan da gwamnati ta janye tallafin man fetur.

Shugabannin biyu al Bashir da kuma Kiir sun kuma yi alkawarin kai hankali nesa a kan rikicin yankin Abyei da ke tsakaninsu, a inda za su kafa rundunar 'yan sanda ta hadin guywa a yankin kafin a kai ga tantance bangaren da ya mallakeshi.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Umaru Aliyu