Cuɗayya tsakanin baƙi da Jamusawa | Labarai | DW | 12.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cuɗayya tsakanin baƙi da Jamusawa

Nan gaba a yau ne shugabar gwamnatin Jamus Angeller Merkell, zata ƙaddamar da tsarin da ta ɓullo da shi, a game da ƙarffafa cuɗe ni in cuɗe ka, tsakanin Jamusawa da baƙi mazauna Jamus.

Merkel zata gabatar da wannan tsari, a wani babban taro da zata jagoranta, a birnin Berlin, wanda zai haɗa wakilai daban-daban, na al´ummomi baƙi mazauna Jamus.

To saidai tunni, wasu ƙungiyoyin turkawa, wanda su ne baƙi mafi yawa a nan Jamus, sun bayyana ƙauracewa wannan taro, a dalili da adawar su, da saban tsarin.

A jimilce Jamus na da baƙi kimanin milion 15, sannan a nahiyar turai, ita ke riƙe da matsayi na 2, bayan France ta fannin yawan musulmi baƙi, mussaman turkawa.

Saban tsarin na shugabar gwamnatin Jamus, ya tanadi ƙara matsa ƙaimi wajen koyan halshen jamusanci, wanda shine tushen farko, ga duk mutumen da ke da burin zama a wannan ƙasa.

Gwamnati ta ware tsabar kuɗi Euro milion 750, domin koyar da jamusanci ga baƙi.

Kamar yadda saban tsarin ya tanada, ya zama wajibi mutum ya iya halshen zamusanci , ya kuma kasance da aiki ƙwaƙƙwara, kamin ya samu damar kawo iyalin sa a ƙasar Jamus.

Wannan mataki ya jawo mumunar suka, daga ƙungiyoyin baƙi jamusawa.