1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

CSU ta samu koma-baya a zaben jihar Bavaria

Ahmed Salisu
October 14, 2018

Jam'iyyar CSU ta Horst Seehofer da ke kawance jam'iyyar CDU ta Angela Merkel ta samu koma-baya a zaben gama-gari da aka yi a jihar Bavaria da ke kudu maso gabashin tarayyar Jamus.

https://p.dw.com/p/36X7i
Landtagswahl in Bayern
Hoto: Getty Images/AFP/C. Stache

Sakataren jam'iyyar CSU mai mulki a jihar ta Bavaria Markus Blume ya bayyana cewar jam'iyyarsu ta rasa rinjayen da take da shi bayan sakamakon farko da ya fita na zaben gama-gari da aka yia  jiahar a wannan Lahadin.

Sakamakon dai ya nuna cewar jam'iyar ta CSU da Horst Seehofer ke jagoranta ta samu kashi 35.3 cikin 100 wanda ba karamin koma baya ne ga jam'iyyar a jihar wadda ke zaman inda ta fi karfi a kasar.

A daura da wannan koma-bayan da CSU din ta samu, ita kuwa jam'iyyar The Greens ta masu rajin kare muhalli ta samu cigaba ne domin kuwa sakamakon da ta samu na kashi 18.5 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada ba ta taba samunsa kwatankwacinsa ba a jihar.

A share guda jam'iyyar nan ta AfD da ke kin jinin baki ta samu kashi 10.9 cikin 100 yayin da jam'iyyar SPD ita kuma ta samu kashi 9.9 cikin 100 wadda hakan ita ma kamar CSU babban koma baya ne gareta duba da irin sakamakon da ta samu a zabuka shekarun baya.